Peter Obi ya dauki alkawarin yin aiki da kudin danyen man da aka hako a Bauchi don ciyar da Bauchi da Arewa gaba Dan takarar na LP, ya bayyana haka a taron gangamin yakin neman zaben da ya gudanar a Bauchi ranar Alhamis Mr Obi ya kuma bukaci shugabannin kasar nan da su yi koyi da Tafawa Balewa wajen gudanar da mulkinsu don bunkasa Najeriya 

Bauchi - Dan takarar shugabancin kasa a jam'iyyar LP, Mr. Peter Obi, ranar Alhamis, ya tabbatarwa da alummar Jihar Bauchi cewa za ayi amfani da danyen man fetur din aka samu a jihar don ciyar da jihar da kuma yankin Arewa gaba. Ya yi alkawarin ne a yakin neman zaben zaben jam'iyyar da ya gudana a filin wasa na Tafawa Balewa a Bauchi, babban birni Jihar Bauchi, a yankin Arewa maso gabashin Najeriya. 

Mun san abin da yake faruwa a Bauchi a halin yanzu. Muna son yin amfani da danyen man da aka hako don cigaban Bauchi, da kuma baku ayyukan yi. Zamu tabbatar anyi amfani dashi don cigaban Bauchi, da cigaban Arewa, don tabbatar da komai yana aiki bawai mutum daya ya sace kudin yabar kowa a cikin yunwa ba. 


Previous Post Next Post