Yunkurin iyalan gidan marigayi Janar Sani Abacha na kokarin dakatad da binciken kudaden da ake zargin mahaifinsu ya wawura lokacin mulkinsa ya sake gamo da tangarda Kotun kolin Najeriya ta yi watsi da karar da babban 'dansa Mohammed Abacha ya shigar na hana gwamnati sake bude takardar bincike Alkali Emmanuel Agim na kotun kolin Najeriya ya ce karar bata da wani gaskiya cikinta.
Abuja - Gwamnatin tarayya ta samu nasara a kotun Allah ya isa kan iyalan marigayi tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Janar Sani Abacha,, bisa zargin da ake musu na hannu cikin wawuran kudin kasa da mahaifinsu yayi. Gwamnati na son kwato wasu makudan miliyoyi da ake zargin marigayin ya boye a wasu kasashe irinsu Amurka da Bailiwick of Jersey.
Hukuncin kotu Alkalan kotun kili karkashin jagorancin Alkali Emmanuel Agim, sun yi ittifakin cewa bincike ya nuna gaskiya cikin bukatar da iyalan Abacha sukayi. Saboda haka ya yi watsi da karar kuma hakan ya bawa gwamnatin daman cigaba da tuhumarsu, rahoton The Nigerian Tribune.