Kotun sasanta rikicin ma'aikata a yau Laraba, ta kori hukuncin sashi na 127 na rundunar 'yan sandan Najeriya na 2020 da ya buƙaci korar wata jami'ar 'yar sanda da ta yi ciki ba tare da aure ba.
'Yar sandar mai suna Omolola, ta kalubalanci korarta a kan zargin cewa hukumomin 'yan sanda sun musguna mata tun da ba a kori takwarorinta maza ba da suka aikata irin laifinta.
Sai dai a wani hukunci da mai shari'a D.K Damulak na kotun sasanta ma'aikata a Akure ya yanke a ranar Alhamis, ya ce bangaren 'yan sandan da ya bukaci ƙorar 'yar sandar da ta yi ciki, yana cike da musgunawa da kuma ba a yi shi bisa ka'ida ba.
A cewar kotun, sashin dokar 'yan sandan, ya saɓawa sashi na 42 na kundin tsarin mulki da kuma sashi na 2 na hukumar ƙare hakkin dan adam wanda ya yi watsi da cin zarafi na jinsi.
Alkalin ya ce dokar ‘yan sanda ba za ta iya tsayawa ba saboda ba ta aiki kan ‘yan sandan da ba su yi aure ba da suka yi wa mata ciki, saboda haka suka yi watsi da ita.
Alkalin ya umurci a biya 'yar sandar diyyar naira miliyan 5 saboda take hakkinta na ‘yancin yin walwala.