Ƴan bindiga sun sace fasinjoji da dama a tashar jirgin ƙasa dake ƙaramar hukumar Igueben, jihar Edo.
Fasinjojin na jiran zuwan jirgi domin tafiya zuwa Warri cikin jihar Delta lokacin da ƴan bindigan suka kawo musu farmaki. Jaridar Daily Trust ta rahoto.
Har ya zuwa yanzu ba a samu tabbaci ba kan cewa ko wani ya rasu a yayin harin amma wasu daga cikin matafiyan sun samu raunika, kamar yadda kakakin hukumat ƴan sandan jihar Edo, Chidi Nwabuzor ya tabbatar.
A cewar sa, ƴan bindigan waɗanda ke ɗauke da bindigu ƙirar AK 47, sun farmaki tashar jirgin ƙasan ne a yammacin ranar Asabar inda suka yi ta harbin iska kafin daga bisani suka yi awon gaba da matafiyan.
A ranar 7 ga watan Janairun 2023, da misalin ƙarfe huɗu na yamma, ƴan bindiga ɗauke da bindigu ƙirar AK 47 sun farmaki tashar jirgin ƙasan dake a Igueben, jihar Edo sannan suka sace fasinjoji da dama waɗanda ke jiran zuwan jirgi domin tafiya zuwa Warri.
Ƴan bindigan waɗanda suka yi ta harba bindiga a sama sun ji wa wasu mutane raunika. Tawagar jami’an ƴan sanda da sauran hukumomin tsaro na Edo sun ziyarci inda lamarin ya auku domin kare lafiya d dukiyar sauran fasinjojin.
Tuni har an fara bin sawun ƴan bindigan domin a cafko su. A cewar sa
Wannan lamarin na zuwa ne ƙasa da shekara ɗaya bayan ƴan bindiga sun harbe wasu fasinjojin jirgin ƙasan Kaduna sannan suka sace fiye da mutum 60 daga cikin su.
Lamarin da ya tilasta gwamnatin tarayya dakatar da zirga-zirgar jirgin ƙasan Abuja-Kaduna har na tsawon wata shida.