Sarkin Musulmi a Najeriya, Alhaji Sa’ad Abubakar III, ya gargaɗi 'yan siyasan kasar nan su guji zage-zage da aibata juna Mai Alfarma Sarkin ya yi wannan gargaɗi ne yayin da Atiku Abubakar, ɗan takarar shugagan kasa ya kai masa ziyara fada Shugaba a Addinin Musulunci ya ce ya zama wajibi mutane su guji ayyukan da zasu gurbata masu rayuwarsu ta lahira 

"Duk abinda zaka yi ka ji tsoron Allah, idan ka yi imani Allah ke bayarwa kuma ya hana to zaka samu nasara kuma zaka yi kyakkwan karshe. Wannan rayuwar kalilan ce dole mu yi aiki domin rayuwar lahira." 

Ya kuma bayyana cewa, Tinubu na da bunu a kaba, don haka zai abubuwa marasa dadi ga ‘yan Najeriya idan aka zabe shi. A cewarsa: “Wannan ba siyasar kiyayya bace, siyasa ce ta ba da kariya. Siyasa ce ta tsare lafiyar kasa kuma aiki ne na ‘yan kasa. “A tsarin shugabanci, babu shugaban da zai jagoranci mutane zuwa inda bai taba zuw aba. Wannan mutumin zai samar da abin da shi kansa yake ne, ba wai abin da yake ya yi ba. Duniya ta san waye shi kuma mu ma mun sani.” 


Previous Post Next Post