Labari Da Ɗumi Ɗumi: “Za’a dawo da gawar Fir’auna Najeriya”

Wani ɗalibi mai suna Ashrab Al-Hazard dake karatu a jami’ar al’azhar ta ƙasar masar ya ce ya kamata a ɗauko gawar Fir’auna daga ƙasar Masar wato Egypt a dawo da ita Najeriya.


Saboda nan ne tafi dacewa a adana ta domin kuwa kusan dukkan ƴan Najeriya kashi 85 basu da gaskiya da kuma tausayin junansu.

Ɗalibin ya bayyana cewar babu inda ake tafka rashin tausayi kamar ƙasar Najeriya kamar yadda ya rubuta a shafinsa na Instagram.
Previous Post Next Post