Kalli Sabuwar kyakkyawar jarumar kannywood A'isha Yusuf jolina Wacce ta fito daga kasar Niger
Mutane suna Tofa albarkacin bakinsu akan wannan jarumar inda a gefe guda wasu ke cewa waisu kannywood yanzu Basu da wasu jarumai masu kyau sai wadanda suka fito daga kasar Niger duk jaruman nasu masu kyau sun Kare inda wasu Kuma sukayi aure.
Wannan sabuwar jaruma ta fito da Farin jini domin kowa yabonta yakeyi, saboda yadda mutane sukaga kamun ludayinta inda aka gano cewa Tana da hankali da Kuma kamun kai, sai dai Kuma wata Karin magana da hausawa suke cewa "Ba'a yabon dan kuturu sai ya shekara da yatsu"