A satin daya gabata ne muka kawo muku labarin yadda Murja Ibrahim Kunya tayi murnar cikan mabiyanta na shafin Tiktok miliyan 1.

Bayan bayyana zata hada taro domin a tayata murna,sai kwatsam muka sami labarin dake fadin cewa an rufe account din jarumar ta Tiktok din.

Daman shi rufe account (Banning) yana kasancewa ne idan mutum ya aikata wani abu na ba daidai ba,ko kuma ketare dokokin su.


Murja din dai yanzu haka ta bayyana bata damu ba domin ta yarda hakan kaddara ce ta sameta kuma tana shirye data karbeta a kowanne hali ta sameta.

Ba tare da bata lokaci ba zaku iya kallon cikakken bidiyon anan kasa, kuci gaba da kasancewa damu domin samun labarai da dumidumin su, mungode

 

Previous Post Next Post